11 Disamba 2021 - 13:37
Najeriya: Kungiyar ECOWAS Za ta Gudanar Da Taron Koli A birnin Abuja

A gobe lahadi 12 ga watan Disemba ne shawagabannin kungiyar habaka tattalin Arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS za su gudanar da taron koli da suka saba a babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Ana saran shuwagabannin za su yi bayani game da batutuwa daban –daban da suka shafi ta’addanci rikice-rikice da tsattsauran ra’ayi a yankin, da kuma batun fara aiki da takardar kudi ta bai daya, da kuma batun rikicin siyasar kasashen Guinea da Mali da ka yi juyin mulki.

A watan day a gabata ne kungiyar ta Ecowas ta kakaba takunkumi kan jagororin juyin mulkin kasar mali da ya hada da takaita yawan tafiye –tafiye da kuma rike dukkan kadarorin manyan jami’an gwamnatin kasar,

Sai dai tun a jiya juma’a ministocin harkokin wajen kasahen kungiyar suka gudanar da taron share fage domin tattaunawa kan wasu batutuwa kafin fara babban taron kolin.

342/