Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Da yake bayani a gefen taro kan tsaro da zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afirka ta shirya a Oran, ya ce kulla hulda da HKI mataki ne da bai dace ba, kuma sadaukar da alummar yankin Arewacin Afirka ne da kuma dora hankin kan hanyar da bata dace ba.
Ya kara da cewa kula dangantaka da kasar Moroko ta yi da gwamnatin yahudawan sahyuniya ya taimaka sosai wajen fadada ikon Isra’ila a Afirka , kuma duk wani mataki da gwamnatin kasar Moroko ta ke dauka a dangatakar soja da Isra’ila yana kara nisanta su ne daga Al’ummar Algeriya.
Kasar Aljeriya tana daya daga cikin kasashen larabawa da suka dake kan nuna goyon bayansu ga alummar falasdinu da kuma adawa da Isra’ila , kuma Lamamra ya bukaci kasashen larabawa da su nuna goyon bayansu ga Falasdinu mai makon goyon bayan Isra’ila ta rika kara baza ikonta a yankin.
342/