Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a birnin Vienna na kasar Austria, shugaban tawagar Iran a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliya Ali Bagheri Kani ya bayyana cewa, sun gabatar da shawarwarin Iran ga wakilan kasashen da halartar tattaunawar, kuma dukkaninsu za su koma kasashensu domin yin shawara.
Ya ce, dukkanin shawarwarin da suka gabatar babu wata kasa wadda ta yi korafin cewa sun saba wa ka’idar yarjejeniyar, amma dai akwai wasu kasashen turai da suka bayyana cewa, shawarwarin na Iran sun sabawa mahangarsu, inda ya ce; haka tana faruwa, kamar yadda su ma za su iya bayar da nasu shawarwarin ya zama sun saba wa mahangar kasar ta Iran.
Ya ci gaba da cewa, abin da yake da muhimmanci shi ne, Iran ta gabatar da shawarwarin ne tare da amincewar kowane bangare, kuma a halin yanzu kowace kasa daga cikin mambobin yarjejeniyar za ta yi nazari kan hakan.
Daga cikin abubuwan da shawarwarin na Iran suka kunsa dai har da janye mata dukkanin takunkuman da Amurka ta kakaba mata baki daya, sannan kuma da dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar, sannan kuma dukkanin mambobin yarjejeniyar su samar da wani tsari wanda zai zama lamuni, wanda zai lizimta msuu yin aiki da dukkanin abin da ke cikin yarjejeniyar, da kuma daukar matakain hana sake maimaita irin abin da Amurka ta yi.
342/