1 Disamba 2021 - 14:14
Hukumar Da ke kula Da Yan Gudun Hijira Falasdinawa Na Fuskantar Matsalar Kudi

Shugaban hukumar majalisar dikin duniya da ke kulada yan gudun hijira Falsdinawa Philippe Lazzarini yace hukumar su ba za ta iya biyan ma’aikata 28000 be a wannan watan saboda matsalar kudade da take fuskanta, kana yayi gargadi game da yi wu war rage yawan muhimman abubuwan da ake yi wa miliyoyin mutane dake cikin mawuyacin hali a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Hukumar tana gudanar da makarantu da Asibitoci kuma tana rarraba kayayyakin abinci ga miliyoyin falasdinawa yan gudun hijira da aka yi rijister sunayensu a fadin gabas tsakiya. Mafiyawancin iyalan falasdinawa ne wadanda Isra’ila ta kora daga gidajensu tun a yakin shekara 1948.

Mafiyawancin falasdinawa yan gudu hijira miliyan 5.7 ne ke zaune a sansanin yan gudun hijira da aka gina shi daga baya sai dai mafi yawancinsu suna rayuwa ne ciki bakin talauci a yankun da isara’ila ta mamaye a gabar yammacin kogin Jodan da gabashin birnin Qudus da yankin Gaza da kuma a kasahen labanon siriya da Jodan.

Falasdinawa sun bayyana cewa yan gudun hijira suna da hakkin komawa kasarsu ta haihuwa da israila mamaye, matakin da mafiyawancin kasashe suke goyon baya, sai dai Isra’ila ta ki amincewa das hi, wanda idan aka yi amfani das hi to mafi yawancin kasar za ta koma hannnun falasdinawa ne.

342/