22 Nuwamba 2021 - 13:18
Libiya : Firaministan Riko Ya Mika Takararsa A Zaben Shugaban Kasa

Firaministan rikon kwarya na Libiya Abdul Hamid Dbeibah, ya ajiye takararsa a zaben shugabancin kasar, duk da cewa dokokin zaben kasar sun haramta masa tsayawa takara.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Dbeibah ya mika takardun nasa ne a hukumance jiya Lahadi kwana guda gabanin cikar wa'adin gabatar da takara.

Bisa tanadin dokar kasar sai firaministan na wucin gadi ya dakatar da ayyukan gwamnatinsa akalla watanni uku kafin ranar zaben da za a gudanar a ranar 24 ga watan Disamba, kafin ya tsaya takara.

Lokacin da ya hau mulki a farkon wannan shekarar, Abdel Hamid Dbeibah ya yi alkawarin ba zai tsaya takara ba.

Abin jira a gani shi ne ko hukumar zaben kasar za ta amince da takararsa a zaben.

342/