18 Nuwamba 2021 - 11:30
Isra’ila Na Goyon Bayan Wasu Yan Takarar Neman Shugabancin Kasar Libiya

Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta na goyon bayan wasu yan takara guda biyu na neman shugabancin kasar Libiya a zaben da za’a yi a watan gobe , da nufin share hanyar kulla hulda tsakaninta da gwamnati mai zuwa,

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Al-akhbar Daily ta kasar Labanon ta fitar da wani rahoto da ke nuna cewa gwamnatin yahudawan sahyuniya ta nuna gamsuwa da wasu yan takarar shugabancin kasar Libiya guda biyu wato janaral Khalifa Haftar da kuma saifil Islam Ghaddafi dan tsohon shugaban gwamnatin kama karya na kasar da aka kashe, a matsayin wadanda za su iya cika mata burinta na kokarin sake kulla huldar Diplomassiya da kasar,

Rahoton ya jaddada cewa : ‘yan takarar shugabancin kasar guda biyu a shirye suke su daidaita alakarsu da Isra’ila kuma zai kasance wani bangare ne daga cikin shirye shiryen da suke yi da ba’a bayyana ba, domin gudun kada lamarin ya shafi kuri’un da za su samu a lokacin zabe, musamman idan aka yi la’akari da yadda al’ummar Libiya suke adawa da kulla hulda da Isra’ila

Wannan yana zuwa ne bayan ziyarar da babban dan Janar Khalifa Haftar wato Saddam ya kai Isra’ila a watan jiya, inda ya gana da jami’an gwamnatin Isra’ila kuma ya nuna gamsuwarsa da batun kulla hulda tsakanin tel aviv da kuma Tripoli , ita kuma ta yi alwashin bawa Libiya duk wani taimakon soji da na siyasa idan har aka daidaita alaka tsakani .

342/