15 Nuwamba 2021 - 17:02
Falasdinu: Likitoci Sun Ce Kayed al-Fasfous Yana Iya Mutuwa A Ko Yaushe Saboda Yajin Cin Abinci Da Yake Yi

Likitoci a wani asbitin da ake jinyar Kayed al-Fasfous, bafalasdine fursina da yake yajin cin abinci, sun bayyana cewa ya na iya mutuwa a ko wani lokaci saboda yajin cin abincin da yake yi wanda ya kai kwanaki 123.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto cibiyar yada labarai na falasdinawa wacce ta nakalto dan uwan Kayed al-Fasfous ya na cewa likitoci a asbitin Barzilai ta haramtacciyar kasar Isara’ila na cewa al-Fasfous ya na fama da karancin ruwa a jiki, kuma jininsa ya fara daskarewa a wasu wurare a jikinsa, don haka akwai yiyuwa ya mu a ko yaushe.

Kayed al-Fasfous dan shekara 34 a duniya ya na yajin cin abinci ne don nuna rashin amincewarsa da tsare shi ba bisa ka’ida ba, wanda jami’an tsaron yahudawan suka yi, ba tare da tuhmarsa ko kuma gabatar da shi a gaban koto ba na lokacin mai tsawo. <p "="">Banda Kayed al-Fasfous dai, akwai wasu Falasdinawa guda 4 wadanda su ma suke yajin cin abinci saboda dalili iri daya da Kayed. Kuma sune Aala Aaraj, wanda yake yajin cin abinci na kwanaki 98, Hesham Abu Hawwash wanda yake yajin cin abinci na kwanaki 89, Ayyad Hureimi wanda yake yajin cin abinci na kwanaki 52 da kuma Lo’ai A-Ashqarwanda yake yajin cin abinci na kwanaki 34.

342/