Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jirgin ya fado ne jim kadan bayan tashinsa daga filin hauwa da saukar jiragen sama na Juba, inda dukkan mutane dake cikinsa suka mutu, kuma ya kunshi 'yan kasar Sudan ta kudu guda daya, sai kuma 'yan kasar Sudan guda biyu da kuma 'yan kasar Ukrain guda biyu. Jirgin mallakin wani kamfanin cikin gida ne kuma yana dauke da ganga 28 na manfetur na hukumar samar da abinci ta Majalisar dinkin duniya dake garin Maban inda aka tsugunar da yan gudun hijira sama da 100,000. Tuni da kungiyar bada agaji ta red Cross ta karbi gawawwakin mutane da suka kone kurmus wadanda ba’a iya tantancesu saboda konewa da suka yi.
342/