Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saeed Khatibzadeh, gwamnatin da ta bayyana aniyarta na sake komawa kan yarjejeniyar nukiliya, amma sai gashi tana cigaba da aiwatar da manufofin tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump na ci gaba da sanya takunkumai, lamarin dake isar da sakon rashin tabbaci.
Ya kara da cewa, gwamantin Amurkar da ta gaji wacce ta shude, ta bayyana gazawarta a fili wajen kasa fahimtar hakikanin yadda Iran take.
Kakakin ya bayyana cewa, duk wani matsin lamba daga Amurka ba zai taba haifar da illa ko sauya manufofin gwamnatin Iran na tabbatar da tsaron kasarta da zaman lafiyar al’ummar kasar ba.
Amurka dai ta sanya takunkumai ne kan wasu kamfanoni da daidaikum jami’an kasar Iran da take dangantasu da shirin kasar na jirage marasa matuka.
342/