25 Oktoba 2021 - 14:28
Ra’isi : Ya Rage Ga Kasashen Turai Da Amurka, Game Da Tattaunawar Vienna

Shugaban kasar Iran Ebrahim Ra’isi, ya bayyana cewa ya rage wa kasashen turai da Amurka game da batun komawa bakin tattaunawar Vienna da aka dakatar yau kusan watanni biyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ‘’Yau abunda ke damun kasashen turai da Amurka shi ne kin daukar matakai, alhali mu mun riga mun dauki namu matakan, saidai matsalar ita ce sauren bangarorin sun gaza daukan matakai, inji shugaban kasar ta Iran.

Iran dai na mai bukatar Amurka ta dage mata dukkan takunkuman da aka kakaba mata tun daga shekarar 2018 a lokacin mulkin tsohon shugaba Donald Trump, wanda ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar ta 2015.

Kasashen turai da Amurka, sun matsu da ganin ta koma bakin tattaunawar Vienna ta neman farfado da yarjejeniyar, a daidai kuma lokacin da Isra’ila ke barazanar daukan matakin soji kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran.

Saidai game da barazanar ta Isra’ila, Iran ta sha alwashin yi wa Isra’ila mummunar barna idan har ta kuskura amfani da karfin soji.

342/