Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kamfanin dillancin labaran kasar Syria ya bayar da rahoton cewa, An tayar da bama -bamai guda biyu a tsakiyar birnin Damascus da sanyin safiyar yau Laraba, inda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane sha hudu a matsayin hari mafi muni da aka kai babban birnin kasar cikin shekaru hudu.
Ya zuwa yanzu babu wani bangare da ya dauki alhakin kai harin, sai dai kuma bayan wani dan lokaci da kai harin, sojojin gwamnatin sun yi luguden wuta akan wasu sansanonin ‘yan ta’adda da gwamnatin Turkiya ke marawa baya a cikin Lardin Idlib da ke kan iyakokin kasashen biyu, wadanda suke da hannu wajen kai wasu hare-haren ta’addancin makamantan wannan a baya.
Kafofin yada labaran Syria sun ce, an kai harin ta'addanci ne ta hanyar tayar da bama -bamai a lokacin wata motar bas da ke dauke da sojoji take wucewa a wata babbar gada a cikin birnin Damascus, a kusa da gidan adana kayan tarihi na kasa da ke tsakiyar babban birnin na Syria.
342/