Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mukaddashin Ministan Harkokin Waje na sabuwar gwamnatin Afganistan da "Taliban" ta kafa, Amir Khan Muttaki, a yayin taron manema labarai da tawagar ta Taliban ta gudanar bayan kammala taron "Moscow Formula", ya jaddada cewa kasashen da ke shiga tattaunawar sun tabbatar da goyon bayansu ga Afghanistan, kuma sun yi alkawarin bai wa kasar taimakon jin kai.
Muttaki ya yi kira ga Amurka da ta saki kudade da kadarori na kasar Afganistan da ta rike, yana mai nuni da cewa, wadannan kudade mallakar mutanen Afganistan ne, kuma sabuwar gwamnati tana da bukatarsu domin biyan mutane albashi, kuma Washington ba ta da hakkin rike su.
Haka nan kuma Ya yi nuni da cewa, dukkan mahalarta taron na Moscow sun bayyana imaninsu kan cewa, rashin tsaro da kwanciyar hankali a Afghanistan "ba zai amfani kowace kasa ba, bilhasali ma hakan yana cutar da su ne.
Ya kara da cewa mahalarta taron sun bayyana aniyarsu ta warware dukkan banbance -banbance ta hanyar tattaunawa, saboda yin fito na fito ko yin amfani da karfi ko barazana ba za su warware matsaloli ba.
342/