18 Oktoba 2021 - 14:42
Abdollahian : Wanzuwar Da’esh A Afghanistan Na Da Matukar Hadari

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdollahian, ya bayyana da babban hadari wanzuwar kungiyar Da’esh a kasra Afghanistan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Abdollahian, na mai Allah wadai da hare haren ta’addancin da da suka faru makwannin baya bayan nan a kasra ta Afganistan, kuma a cewarsa babban hadari ne wanzuwar ire iren kungiyoyin ‘yan takfiriya a wannan kasa.

Ya bayana hakan ne yayin ganawa da sakatare janar na ma’aikatar harkokin wajen kasar Austria, wanda ya ziyarci kasar Iran a ranar Asabar.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran, ya kuma bukaci kasashen turai dasu dubi halin da ‘yan Afghanistan ke ciki da idon rahama, musamman hakkinsu da kuma yin tir da hare hare ta’addancin dake faruwa a kasar.

Mutane sama da 40 ne suka rasa rayukansu a wani hari da kungiyar IS ko Da’esh ta dauki alhakin kai wa a wani masallacin ‘yan Shi’a dake birnin Kandahar a ranar Juma’a data gabata.

342/