14 Oktoba 2021 - 11:46
EU : Ziyarar Jami’in EU A Tehran, Na Da Manufar Farfado Da Tattaunawar Vienna

A wannan Alhamis ce mataimakin babban jami’in kula da harkokin kungiyar tarayyar turai, kana kuma wakilin EU a tattaunawar Vienna kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran zai kawo wata ziyara a nan Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Makasudin ziyarar shi ne tattaunawa da Iran, domin shirya yadda za’a koma bakin tattaunawar Vienna da zumar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.

Yayin ziyarar tasa jami’in na EU, Enrike Mora, zai gana da ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Hossein Amir Abdollahian, da kuma sabuwar tawagar da za ta wakilci Iran a tattaunawar ta Vienna, bayan zuwan sabuwar gwamnatin Ebrahim Ra’asi.

Kafin hakan dai Iran ta bukaci a bata tabacin cewa ba za’a koma ‘yar gidan jiya ba kafin ta koma yarjejeniyar ta 2015, duba da yadda gwamnatin Trump a waccen lokacin ta fice daga cikin yarjejeniyar.

Haka kuma Iran, na mai bukatar a dage ma ta takunkuman da aka kakaba mata.

342/