Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tun Kafin hakan dama, Kenya ta zargi kotun da fifiko.
A jiya Talata ne kotun kolin ta MDD, da ke birnin The Hague ta bai wa Somaliya kaso mafi tsoka na yankin tekun Indiya mai arzikin kifi da yiwuwar arzikin iskar gas da kasar Kenya ta yi ikirarin cewa mallakinta ne.
Cikin hukuncin da ta yanke, kotun ta ICJ ta ce babu iyakar teku da aka amince da ita tsakanin kasashen biyu a baya, amma ta shata wata sabuwar iyaka kusa da inda Somaliya ke ikirarin mallaka, yayin da Kenya za ta ci gaba da rike wani bangare na ruwan da ke tsakanin kasashen biyu.
An yi tsamannin wannan hukunci na babbar kotun ta Majalisar Dinkin Duniya zai kawo karshen takaddamar kan iyaka da aka fara a shekarar 2014 tsakanin Kenya da Somaliya, wacce kuma ke kara dagula alakar da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna a gabashin Afirka.
hukuncin kotun wanda bai da daukaka kara, ba ya tilasta wa kasashen aiwatar da hukuncin.
342/