11 Oktoba 2021 - 12:54
Libiya : Bangarorin Dake Rikici Sun Amince Su Janye Mayakan Ketare

Tawagar aikin wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya ta sanar cewa, sabon zagayen tattaunawar sulhun da aka gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland, tsakanin wakilan dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya, ta haifar da muhimmin sakamako.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tun da farko bangarorin biyu sun cimma matsayar za su janye dakarunsu da kuma na kasashen waje.

Rahotanni sun bayyana cewa, wani kwamitin sojoji na hadin gwiwa wanda ya kunshi wakilai biyar-biyar daga dukkan bangarorin dake yaki da juna a Libya sun kammala taron tattaunawa na tsawon kwanaki uku a Geneva.

Bangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniya da nufin baiwa mayakansu da dakarun kasashen waje damar ficewa daga kasar ta Libya sannu a hankali, kuma bisa tsari.

Wakilan sun bayyana cewa, bayan sun koma Libya, za su tattauna da kasashen da abin ya shafa game da yadda za su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka tsara domin mutunta ikon da kasar Libya ke da shi kan yankunanta.

342/