Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An kiyasta masu zabe kimanin miliyan 25 ne zasu kada kuri’a a zaben na gabanin wa’adi, domin sabunda ‘yan majalisar dokokin kasar.
Zaben, an kira shi ne da zumar biyan bukatun masu boren da ya barke a watan Oktoban 2019.
Masu zanga zangar a waccen lokacin wandanda mafi akasarinsu matasa ne sun koka ne kan matsalar cin hanci da rashawa da rashin aikin yi.
Kafin hakan dai rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a sassa daban daban na kasar, domin baiwa jama’a damar kada kuri’a cikin tsanaki.
342/