Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na jaridar Egypt Today ya bayyana cewa hakan ya faru ne a jiya Litinin a lokacinda shuwagabannin bangarorin biyu suka tattauna wannan batun a Vatican.
A karshen taron dai shuwagabannin manya manyan addinin guda biyu sun sha walwashin aiki tare don yaki da masu tsatsauran ra'ayi a cikin mabiyansu da kuma ci gaba da muhawara tsakanin malaman addinin kirista da addinin musulunci don ganin an rage yawan yake yake da sunan addini a duniya.
Ahmed Attayyid da fafaroma Francis sun kara da cewa za su yi aiki tare da rage rarrabuwar kai tsakanin mabiya addinin guda biyu.
342/