30 Satumba 2021 - 13:22
​Iraki: Dakarun Hashd Alshaabi Sun Halaka Wani Babban Kwamandan ‘Yan Ta’adda

A cikin wata sanarwa da suka fitar, dakarun Hashd al-Shaabi sun ce bangarensu na Operation Salahuddin, tare da hadin gwiwar ‘yan sandan tarayyar Iraki, sun sami nasarar cafke babban kwamnada na ‘yan ta’adda Idris Adnan Ismail wanda ake kira Abu Rahma.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan kasurgumin dan ta’adda dai shi ne ke da alhakin tattara abin da ake kira zakka ga ISIL, an kuma samu nasarar damke shi ne a cikin a yankin Al-Nissan da ke kudancin Tikrit a gundumar Salahuddin.

Dakarun Al-Hashd al-Shabi sun jaddada cewa umurnin wannan aikin zai ci gaba da gudana da irin wannan salon a yin kwanton bauna da ayyukan hana kutsawar kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin birane, domin kauce wa barazanar tsaro ga 'yan kasar Iraki.

Akwai dubban daruruwan dakarun sa kai na hashd Alshaabi da suke gudanar da irin wadannan ayyuka na tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta’addanci a sassa daban-daban na kasar Iraki, wanda hakan ne babban abin da ya dakile ayyukan ta’addanci a kasar.

An dai kafa dakarun sa kai na Hashd Al shaabi ne biyo bayan fatawar da babban malamin addinin muslunci na Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya bayar kan hakan, domin murkushe ‘yan ta’addan daesh a lokacin da suka shigo kasara shekara ta 2014, inda matasa sama da miliyan 4 suka yi rijistar sunayensu domin shiga cikin rundunar, amma dai an dauki dubban daruruwa daga cikinsu bayan tantancewa.

342/