Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Da yake bayani kan kyawawan ɗabi’un Manzon Rahama (S), Jagora (H) ya ce, “Manzo ya yi galaba ne kan maƙiya da kyawawan ɗabi’unsa,” ta hanyar afuwa, tausayi, rahama da yafiya, har ga waɗanda suka cutar da shi. Ya ce, Manzon Allah (S) ne ya kamata ya zama ramzi da ma’auni ga al'ummar Musulmi.
A ci gaba da jawabinsa, ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin Musulmi, in da ya ce, rauni da koma bayan da Musulmi ke fuskanta na da alaƙa da rarrabuwarsu. Ya yi kira ga Musulmi da su dunƙule su haɗa kai ko don maslahar Musulunci, ya ce hakan ne zai dawo wa Musulmi da izzarsu—abin da maƙiyan Musulunci ba sa so, domin rarrabuwar Musulmi ita ce ke amfanar da su.
A ƙarshen jawabinsa, ya bayyana cewa, halin da Musulmi ke ciki a yau zai zo ƙarshe, addini zai kafu daram, sannan ƙarfi da izzar al’ummar Musulmi za su dawo, in sha Allah.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
17/RabiuAuwal/1448
30/08/2026
Ra'ayinka