Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Garin Chittagong mai tashar jiragen ruwa na Bangladesh, tare da zuwan bukin haihuwar Annabi (SAW), ya kasance wurin gudanar da bikin gargajiya na "Julus" tare da halartar jama'a masu ibada da yawa.
A cikin wannan bikin addini wanda aka gudanar cikin yanayi mai cike da farin ciki, manyan titunan garin sun cika da jama'a gwanin ban sha'awa waɗanda da hannayensu rike da tutoci masu launin kore da alluna masu ɗauke da rubutun addini, sun nuna ƙaunarsu ta zuciya ga Annabi Mai Girma (SAW). Yawancin mahalarta da suturar gargajiya, sun ba wa wannan muzahara wani salo na musamman.
Majiyoyin cikin gida sun kawo cewa, saboda wannan lokaci, yanayin garin Chittagong ya canza, kuma yankuna daban-daban, musamman "Qazi Deuri" da kewayenta, sun sami haske mai launuka daban-daban, dora tutoci da tage-tage na ado, wanda ya ba da yanayi na haske. Bayan faduwar rana, hasken gine-gine da tituna ya kara nuna farin cikin ruhaniya na garin.
Sautin salwati da waƙoƙin yabon Annabi a ko'ina cikin hanyar muzahara, ya cika Chittagong da kamshin ruhaniya. Masana harkokin addini sun bayyana "Julus" na Chittagong a matsayin fiye da muzahara kawai, kuma sun kwatanta shi a matsayin alamar sabunta alkawari na Musulmai da koyarwar Annabi da kuma bayyanar soyayya da girmamawa ga tafarkin Annabi Mai Girma (SAW).
………………
Ra'ayinka