Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: A yayin jawabinsa, Jagora (H) ya bayyana cewa, lokacin Mauludi lokaci ne da ya kamata ya zama madubi ga al’ummar Musulmi, domin su waiwayi kansu tare da yin nazari kan yadda suke bin saƙon da Manzon Allah (S) ya zo da shi, da kuma irin al’ummar da ya gina ya bari.
A ci gaba da jawabinsa, Jagora ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’ummar Musulmi, ya ce, haɗin kai ba yana nufin mutum ya yi watsi da fahimtarsa ya koma ga fahimtar wani ba. A maimakon haka, yana nufin girmama fahimtar juna, yin uzuri da kusantar juna. Ya ce, irin wannan haɗin kai zai taimaka wajen kawar da shingayen gaba da ƙiyayya da maƙiya suka sa tsakanin Musulmi.
Asabar ce rana ta huɗu da fara taron Makon Haɗin Kan a Abuja, inda Malamai daban-daban daga bangarorin al'ummar Musulmi suka halarta, tare da gabatar da jawabai akan Maudu'ai daban-daban.
A yau Lahadi da misalin karfe 10:00 na safe ne aka gabatar da jawabin rufewa tare da gagarumin Mauludin Manzon Allah (S) a garin Abuja.
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
16/RabiuAuwal/1448
29/08/2026
Ra'ayinka