Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Makon farko na watan Shahrivar a kowace shekara, lokaci ne da ya dace don yin la'akari da ayyukan gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A wannan shekara, gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana alfahari cewa kwanakin makon gwamnati, sun zo daidai da kwanakin haihuwa biyu mai albarka na watan Rabi’ul-Awwal - tsira da amincin Allah su tabbata a gare su da iyalansu.
Ni a wannan damar ina taya dukkan ma'aikata da masu gudanarwa masu aiki a cibiyoyin gwamnati, musamman shugaban ƙasa mai gaskiya kuma mai kulawa na gwamnati ta goma sha huɗu, murnar zagayowar ranar tare da yi musu fatan alkhairi. Musamman idan aka yi la'akari da kyawawan ayyukan da suka yi, duk da takunkumi da makircin makiya Amurka-Sahyoniyya da ƙara tsananta takunkumi da killacewa, a lokacin yakin mamaya na uku da kuma bayansa, wajen samar da kayayyaki da nau'ukan ayyuka daban-daban da jama'a ke bukata, gyara muhimman wuraren da suka lalace, da sarrafa makamashi. Haka nan ya dace a tuna da shugabannin da suka yi shahada Rajaei da Raisi da firayim minista shahidi Bahonar da ma'aikata da manajoji da ministocin da suka yi shahada a gwamnatocin da suka gabata, kuma a gaba gabansu, jagora mai girma shahidi wanda ya zama shugaban ƙasa na kusan wa'adi biyu, mu girmama su kuma mu yi addu'ar Allah ya daukaka darajarsu da kuma saukar da rahamarsa a garesu.
Samun damar yi wa al’umma hidima da kuma manufofin Jamhuriyar Musulunci, wata ni'ima ce mai daraja da ya kamata a kiyaye ta. A wannan lokaci mai muhimmanci da sarkakiya da "Iran mafi ƙarfi" ke fuskanta, ɗaya daga cikin abubuwan da suka wajaba don cimma wannan buri, baya ga aiki dare da rana da ƙirƙira mai ci gaba, shi ne bayyana da kuma ba da labarin iko da ƙarfin Iran da al'ummarta masoya. Rauni, gazawa, da karancin abubuwa, ba sa buƙatar ba da labari ko haskakawa; a'a, suna buƙatar tsarawa da aiki don magance matsalar. Wani lokaci faɗin rauninmu na gaskiya a lokacin da makiya ke buƙatar samar da kuzari, babban taimako ne a gare su, kuma yana iya sa zukatan abokai da magoya baya su damu kuma su rude su. To, idan masu sauraren waɗannan maganganun na gaskiya su ne kawai jama'a da masu son ci gabanmu, to damuwar za ta ragu. Amma ƙarfi, iko, da abubuwa masu kyau, bisa ga koyarwar Alkur'ani "Amma ni'imar Ubangijinka, ka faɗa," suna buƙatar ba da labari da haskakawa.
Al’ummar Iran masoya, waɗanda a cikin watanni shida da suka gabata suka bayyana ainihin darajarsu a fannoni daban-daban na jihadi da makiya, halartar fage, haɗin kai da zumunci, sun cancanci su samu hidimtawar shugabanni da cibiyoyin hukumomin da ke da alhaki a Jamhuriyar Musulunci a kan hanyar zuwa matakin da ya dace na wannan tsari mai tsarki da kuma darajar al'ummar da aka tayar.
Babu shakka, abin da zan faɗa a ƙasa yana cikin manyan shirye-shiryen gwamnati mai hidima ko kuma a cikin jerin manufofinta, kuma ambatonsa a nan don tunatarwa ne kawai. Daga cikinsu akwai wajabcin yin la'akari da jerin matsalolin tattalin arziki - rayuwa kamar hauhawar farashi, rashin aikin yi, sarrafa farashi da kasuwar kayayyaki da ayyuka, da kuma kulawa ta musamman ga wasu abubuwa na fannin tattalin arziki kamar bunkasawa, ƙara zuba jari da jagorantar shi zuwa ga mai amfani da ake bukata, bunƙasa samarwa, sauke darajar dalar a hankali daga matsayinta mai muhimmanci, da kuma mayar da hankali kan tsarin manufofin tattalin arzikin gwagwarmaya. Babban mabuɗin a wannan fanni don magance duk waɗannan batutuwa shi ne dogaro da samarwa na cikin gida. Tabbas, samar da isassun kayayyaki na jama'a da na musamman wata larura ce da ba ta da makawa, wanda idan aka yi la'akari da shi, a wuraren da samarwa na cikin gida bai isa ba, dole ne a yi amfani da shigo da kayayyaki da kyau kuma cikin hikima.
A zahiri, ƙarfafa samar da kayyaki tare da sarrafa shigo da kayayyaki da farashi na iya haifar da yanayin da tabbai masu duhu a fuskar tattalin arzikin ƙasar za su ƙara ƙanƙanta har su kai ga ɓacewa gaba ɗaya. A wannan fagen, ko da yake halin makiya a yaki da bayansa ba shi da tasiri, amma sarrafa abubuwan wannan fage cikin hikima, da neman taimako a wasu lokuta daga jama'a, a wasu kuma daga ƙwararru da masu fasaha, da kuma aiwatar da sabbin damarmaki, za su jagoranci ƙasar zuwa fadada ayyuka da ci gaba.
Makiyan wannan al'umma suna ƙoƙarin sanya mutane su gaskata cewa hanyar ci gaba ta ratsa ta hanyar bin su da kuma buƙatunsu na rashin adalci; yayin da kallon abin da suka yi wa wannan ƙasa da albarkatunta a shekarun da suka gabata, har ma shekaru kafin juyin juya halin Musulunci, ya nuna akasin haka.
Kuma daga cikin muhimman batutuwa akwai amfani da fasaha da sabbin batutuwa da ƙwararrun matasa suka ba da shawara. Wani lokaci amfani da wannan damar a lokacin da ya dace da kuma barin al'ada da halaye na yau da kullun a wani fanni, na iya haifar da ci gaba mai tasiri a kan hanyar haɓaka da ci gaban ƙasar. Wannan yana iya yiwuwa a kowane nau'in samar da iko kamar noma, masana'antu, al'ada da tarbiyya, harkokin sadarwa da zamantakewa.
Kuma daga cikin muhimman batutuwan ƙasar da ya kamata koyaushe su kasance a kang aba ga gwamnati da ma'aikatanta da dukkan masu alhaki da sassan gwamnati, akwai kiyaye haɗin kai da lura da haɗin kan zamantakewa. Duk wani mataki a kowane fanni na al'adu, zamantakewa, siyasa, tsaro, da tattalin arziki dole ne a yi shi tare da la'akari da abin da ya shafi haɗin kan zamantakewa. Wasu ayyuka waɗanda a fili suke da magoya baya a tsakanin wasu sassan ƙasar, idan wannan abin bai shafi su ba, ko kuma abin da aka tsara a matsayin abin da ya shafi su ya zama ba a kula da shi ba a aikace, na iya haifar da illa ga waɗannan sassan da sauran su. Babu shakka, duk wata magana mai karya fata da raunana kuzarin ƙasa da jama'a, da duk wani nau'in rarrabuwa na wahami kamar yanayin yaki ko tattaunawa, haɗin kai ko tsattsauran ra'ayi, sulhu ko neman yaki, wanda a baya ya jawo illa kai tsaye ko a kaikaice ga al'ummarmu masoya, a nan gaba ma yana iya yin tasiri iri wancen. Don haka ina faɗa da Babbar murya cewa, aikata duk abin da zai cutar da haɗin kan zamantakewa, haramun ne.
Kuma daga cikin muhimman batutuwa akwai la'akari da dabaru na farko ga al'adu, ilimi da tarbiyya. Ma'anar dabaru na farko ita ce, tsara sauran dabaru dole ne a yi shi tare da la'akari da wannan batu. A wannan fanni, kulawa ga sassan da ke tushen yada al'ada mai kyau da ingantacce kamar malamai a ilimi da tarbiyya da jami'a da makarantun addini, da kuma ma'aikatan jinya da likitocin da suka sadaukar da kansu don yin ayyukansu a cibiyoyi masu zaman kansu, yana da muhimmanci na musamman; kamar yadda kuma kulawa ga matan gida masu aikin gida, waɗanda suke koyar da mafi kyawun abubuwan al'ada mai kyau ga kowane ɗa a cikin gidajensu, ita ma tana da irin wannan muhimmanci.
Da fatan cewa aiwatar da waɗannan batutuwa da sauran abubuwa masu amfani da ake iya samu a cikin shirye-shiryen gwamnati, zai jagoranci ƙasarmu abar kauna zuwa ga matsayin "Iran mafi ƙarfi", kuma ya sa masu aiki a wannan hanyar su cancanci kulawa ta musamman daga Jagoranmu (Allah ya gaggauta zuwansa) da kuma addu'ar alkhairi da albarka da shiryarwa a gare su.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuh
Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i
6 Ga Shahrivar, 1405
15/Rabu’ul Auwal/1448
28/08/2026
………………….
Ra'ayinka