Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : kasar Iran ya n akalto Mohammad Eslami shugaban hukumar shirin nukliyar kasar Iran ya na fadar haka a safiyar yau Talata a birnin Moscow.
A lokacinda yake maida martani ne ga gwamnatin kasar Amurka wacce ta bayyana cewa dole Iran ta kyale hukumar IAEA ta ci gaba da sanya ido kan ayukanta na makamashin nukliya ko kuma a dora mata takunkumi a hukumar IAEA.
Labarin ya kara da cewa Eslami zai gana da manya-manyan jami’an gwamnatin kasar Rasha, da kuma wata ganawa ta musamman da Alexey Likhachev shugaban hukumar makashin nukliya ta kasar Rasha “ROSATOM”.
342/