28 Satumba 2021 - 07:49
Hamdok: Rikicin Sudan Na Siyasa Ne Ba Na Soji Da Fararen Hula Ba

Firayim Ministan Sudan Abdullah Hamdok ya ce rikicin kasar ba rikici ne tsakanin sojoji da farar hula ba, illa gwagwarmaya tsakanin masu imani na ra’ayin sauyin dimokuradiyya na farar hula, da masu neman toshe hanyar ci gaba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cikin wata hira da gidan talabijin na Sudan, Sudan Abdullah Hamdok ya bayyana cewa "hadin kan dakarun juyin juya hali shi ne sirrin tabbatar sauyi, da samun kariya daga duk wata barazanar da za ta iya kawo cikas ga juyin juya halin Sudan."

Ya yi kira ga dukkan bangarori da su "yi biyayya ga kundin tsarin mulki, da nuna kishin kasa wanda ke ciyar da bukatun kasar da mutanenta a gaba."

Ya ci gaba da cewa, "Kwamitin karfafawa yana daya daga cikin nasarorin juyi, kuma kare shi aiki ne da ya rataya kan kowa, kuma babu ja da baya wajen tabbatar da cewa an bayar da kariyar da ta kamata ga gwamnatin rikon kwaryar kasar, domin kuwa ita ce rufin asirin kowa a kasar a cewarsa.

Kuma ya kara da cewa, "Ina maraba da duk wani korafi daga dukkan bangarorin game da shirye-shiryen gwamnatin, kuma ina sake nanata cewa zan yi aiki tukuru a cikin kwanaki masu zuwa don ciyar da kasa shi gaba."

342/