Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Kwamitin shirya bikin na bana, ya ce za’a gudanar da bikin a cikin kasashe 60 na duniya, inda za’a baje kolin kayayakin tsaro na soji iri daban daban da Iran take da su.
Kamar dai kowace shekara, rundunonin sojoji da jami’an tsaron kasar Iran kan gudanar da gagarunmin fareti tare kuma da nuna wasu daga cikin muhimman abubuwa na ci gaba da kasar ta samu ta fannin tsaro da kuma kariya.
Bikin dai ya samo asali ne bayan kawo karshen kallafafen yakin shekaru takwas da tsohuwar gwamnatin Saddam Hussein, ta kaddamar kan Iran a tsakanin 1980-1988.
Dama ce kuma ta tunawa da shahiddan da suka rasu yayin yakin.
Bisa jajircewa sakamakon kiran mirigayi Imam Khomeini, wanda ya asassa Jamhuriyar musulinci ta Iran, al’ummar kasar sun yi tsayin daka wajen kare kasarsu daga mamayar tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Hussein wanda a waccen lokacin yake samun goyan bayan kasashen yammcin duniya.
Yakin lokacin dai ya yi sanadin shahadar, ‘yan Iran dubu 225 da 570, kuma wasu dubu 574 da 101 sun zama nakasassu.
342/