Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Haka zalika kungiyar Hamas ta dora alhaki kan HKI game da dukkan abin da ya biyo baya sakamakon wannan mummunar siyasar Azabatarwa da ta bullo da shi idan ta kuskura wani daga cikin fursunonin ya rasa ransa, don haka ta bukaci HKI ta saki dukkan fursunonin da take tsare da su.
Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun zargi Isra’ila da take hakkokin Falasdinawa da take tsare da su wadda yarjejeniyar Janeva ta hudu ta ba su, sama da Plasdinawa 7,000 ne suke tsare a gidajen yarin HKI, a yayin da daruruwa daga cikinsu, ana tsare da su ne karkashin sabon tsarin tsare-tsare ne da ta bullo da shi.
Wanna matakin yana zuwa ne bayan da wasu fursunoni Palasdinawa suka tsere daga gidan yarin mafi tsaro na HKI, kafin daga bisani a kara kama wasu daga cikinsu.
342/