17 Satumba 2021 - 10:29
Iran Ta Kaddamar Da Cibiyar Yin Allurar Rigakafi Mafi Girma Da Za’a Yi wa Mutane 3500 Kullum

Tun bayan da aka fara gudanar da rigakin Cutar Annoba Korona a fadin kasar Iran an bude babbar cibiyar mafi girma a kasar da za’a rika yi wa mautane sama da 3500 Allurar rigakafin a kowacce rana , kuma za rika aiki cikin saoi 24 ne, nan da makon gobe za’a kara bude cibiyar yin Allurar ta 4 a birnin Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Da yake bayani a wajen bude cibiyar shugaban kwamitin yaki da cutar Korona a Iran Ali Riza Zali kuma kwamandan dakarun kare juyin musulunci na kasar Iran ya fadi cewa wannan Ita ce cibiyar yin Allurar rigakafi mafi girma da aka bude a kasar da za’a rika yi wa mutane sama da 3500 Allurar rigakafin a kowacce rana kuma ana saran ya kai mutane 10,000 a nan gaba,

Shigo da Allurar rigakafin da aka yi daga kasashena waje ya taimaka sosai wajen kara saurin yin rigakafin , inda ya zuwa jiya da yamma an yiwa mutane sama da 6825000 Allurar zango na farko, yayin da sama da mutane 2930,000 kuma aka yi musu zango na biyu,

342/