12 Satumba 2021 - 13:10
Firaministan Iraki Na Ganawa Da Hukumomin Iran

Firaministan Iraki, Mustafa al-Kadhimi, ya fara wata ziyara a Tehran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : M. al-Kadhimi, wanda ke jagorantar wata babbar tawagar ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa, an tsara zai gana da shugaban kasar Iran, Ebrahim Ra’isi. Bangarorin zasu tattauna kan batutuwan da suka shafi alakar dake tsakanin kasashen biyu, da yankin har ma da batutuwan da suka shafi kasa da kasa.

A karshen watan Agusta da ya gabata, ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amirabdollahian, ya halarci taron kasa da kasa na Bagadaza kan samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Dama dai sabuwar gwamnatin ta Iran, ta bayyana cewa zata fifita alaka da kasashe makobtanta.

342/