11 Satumba 2021 - 11:55
Marocco: An Nada Aziz Akhannouch, A Matsayin Shugaban Gwamnati

Sarkin Marocco Mohammed VI, ya nada, Aziz Akhannouch, a matsayin sabon shugaban gwamnatin kasar, wanda aka damkawa amanar kafa sabbin mambobin gwamnati.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Matakin nadin da akayi wa attajirin Aziz Akhannouch, na zuwa ne bayan da gungun jam'iyyun adawa na kasar suka yi rinjaye a zaben ‘yan majalisun dokokin kasar.

A Marocco dai shi ne karon farko da jam'iyyar PJD ta masu matsakaicin kishin addini da ke mulkin kasar, ta sha mummunan kaye a zaben 'yan majalisun dokoki.

Gungun jam'iyyun 'yan adawa ne dai suka kawo karshen rinjayen da jam'iyyar take da shi.

342/