9 Satumba 2021 - 13:25
​Iran: Mummunan Halayen Hukumar IAEA Zai Hana Samun Hadin Kan Da Ake Bukata Da Kasashen Turai

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya gargadi hukumar IAEA kan irin mummunar mu’amalarta da kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA :Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban ya na fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarko da shugaban majalisar tarayyar turai Charles Michel a jiya Laraba.

Shugaban ya kara da cewa Iran ta na son nuna gaskiya a mu’amalarta da hukumar IAEA amma halayen da hukumar take nunawa, ya bayyana cewa bata cancanci hadin kan da Iran take bayarwa ba.

Sau da dama hukumar takan gabatar da bukatar binciken wasu wurare a kasar Iran bisa rahotannin da ta karba daga hukumomin leken asiri na Amurka da HKI, duk da cewa an haramta mata yin hakan. Amma Iran takan basu dama su gudanar da binciken don kyautata dangantaka ta ita, amma duk da haka hukumar ta na sake nanata irin wannan bukatar.

Daga karshe shugaban ya kammala da cewa Iran ce kadai take aiki da yarjejeniyar JCPOA, banda Amurka da kasashen turai wadanda suka rattabawa yarjejeniyar hannu.

342/