9 Satumba 2021 - 13:22
​Morocco: Jam’iyyar RNI Ta Lashe Mafi Yawan Kujeru A Majalisar Dokokin Kasar

A zaben majalisar dokokin da aka gudanar a kasar Morocco a jiya Laraba, jam’iyyar RNI ta lashe mafi yawan kujeru a majalisar, biye da ita akwai jam’iyya PAM sannan jam’iyyar PJD ta masu kishin addinin ta sami kujeru 8 a majalisar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA :Wannan dai shi ne sakamakon farko na zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar a kasar ta Morocco a ranar jiya Laraba.

Jam’iyar RNI wacce wani hamshakin attajiri kuma tsohon ministan noma na kasar, Aziz Akhannouch yake jagoranta ta sami kujeru 97 daga cikin kujeru 395 na majalisar dokokin kasar, biye da ita akwai Jam’iyyar PAM mai kujeru 82 daga nan sai jam’iyyar Istiqlal mai kujeru 78. Jam’iyyar PJD dai ta sami kujeru 8 ne kacal bayan an irga kashi 96% na kuri’un da aka kada.

342/