8 Satumba 2021 - 13:44
​Janar Qa’ani Ya Yi Gargadi Dangane Makircin Amurka Na Hada Rikici Sunna Da Shi’a A Afganistan

Babban kwamandan dakarun Quds na dakarun juyin juya halin musulunci a nan Iran Burgediya Janar Esma’il Qa’ani, ya yi gargadi dangane da makircin Amurka na hada mabiyan mazahabar shi’a masu rinjaye a Iran da kuma mabiya mazhabar sunan masu rinjaye a kasar Afganistan. Don haka ya bukaci a warware matsalolin da kasar Afganistan take fama da su a halin yanzu ta hanyar samar da gwamnati wacce dukkan yan Afganistan za su sami wakilci a cikinta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, Janar Qa’anin ya gana da kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar Iran a jiya Talata a asirce, inda ya bayyanawa kwamitin yadda ya ke fahintar rikicin kasar Afganistan a halin yanzu., musamman bayan karbar Taliban iko da kasar.

Kakakin kwamitin tsaro na majalisar dokokin kasar Iran, Seyyed Nizamuddin Mousawi ya fadawa ‘yan jarida bayan taron na jiya, kan cewa matsayin Iran dangane da abinda ya ke faruwa a kasar Afganistan a fili yake, kuma shi ne matsayin Imam Sayyid Aliyul Khamina’i Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar, kan cewa Iran ba za ta nada hannayenta ta na kallon al-amura suna tabarbarewa a makobtanta na gabas ba.

Don tsaro da zaman lafiya a kasar Afganistan, shi ne tsaro da zaman lafiya a kasar Iran.

342/