20 Satumba 2026 - 23:58
Source: ABNA24
Sheikh Ahmad Qabalan: Ƙasashen Larabawa Da Musulmi Su Ɗauki Mataki Don Cimma Yarjejeniya Ta Haɗin Gwiwa Mai Ƙarfi

Sheikh Ahmad Qabalan, Babban Mufti na Ja'afariyya na Lebanon, a cikin wani saƙo da ya aikewa wa ƙasashen Larabawa da Musulmi, ya nanata cewa a cikin yanayin da yankin ke ciki a yanzu da kuma rikicin da ke cikin tsarin ƙasa da ƙasa, waɗannan ƙasashe ya kamata su ɗauki mataki don cimma yarjejeniya ta haɗin gwiwa mai ƙarfi domin ƙoƙarin Amurka na haifar da fitina da rikici a tsakaninsu ya ci tura.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Shaikh Qabalan ya ce: ƙasashen Larabawa da Musulmi suna da haɗin kai a cikin muhimman muradunsu da asalinsu kuma wajibi ne su ɗauki mataki don samar da tushen yarjejeniya ta Larabawa da Musulmi domin hana su zama fagen rikici, sayen makamai da lalacewa.

Ya roƙi Pakistan, Iran, Saudi Arabiya, Turkiyya, Iraki, Masar da Yemen da su yi gaggawa wajin samar da wannan yarjejeniya kuma su sanya tushenta ya zamo "haɗin kai na imani na gaskiya, nesa da sheƙar Shaidanun Washington da Tel Aviv."

Qabalan ya bayyana cewa Amurka da Isra'ila su ne tushen rikice-rikicen yankin kuma Washington tana amfani da sabanin da ke tsakanin ƙasashen Larabawa da Musulmi don kiyaye tasirinta.

A ƙarshe ya roƙi ƙasashen Ƙungiyar Haɗin Gwiwar Tekun Farisa da su fahimci sabon yanayin yankin kuma ya nanata cewa duk wani dogaro kan nasarorin da suka samo asali daga rawar Amurka na iya samun babban sakamako ga Gabas ta Tsakiya.

…..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha