Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, akalla mutane 17 ne aka tabbatar ad mutuwarsu wasu da dama suka samu raunuka sakamakon harbe-harben da mayakan Taliban suka yi a birnin Kabul da bindigogi, saboda murnar kwace iko da wasu yankunan Panjshir wadanda suka ki amincewa da mulkin Taliban.
Wanann na zuwa ne bayan bayanan da majoyoyin kungiyar suka bayar ne na kwace iko da yankin na Panjshir, amma Ahmad Mas’ud da ke yin turjiya a gaban mayakan Taliban, ya karyata labarin, inda ya ce suna nan suna artabu mayakan Taliban da kuma mayakan Alka’ida da suke mara wa Taliban baya.
A wani rahoton kuma da kamfanin dilalncin labaran na Reuters ya bayar, sheda cewa ya nakalto daga muhimman majiyoyin kungiyar ta Taliban cewa, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Mulla Abdulganiy Baradar ne zai jagoranci sabuwar gwamnati da za a kafa a kasar Afghansitan.
Rahoton ya ce, bisa ga abin da majiyoyin kungiyar suka tabbatar, Mulla Muhammad Ya’akub, dan tsohon shugaban kungiyar Taliban Mullah Umar, da kuma Shir Muhammad Abbas, za su rike wasu manyan mukamai a cikin gwamnatin da za a kafa.
Mulla Baradar dai ya koma kasar Afghanistan ne bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar a ranar 15 ga watan Agustan da ya gabata, bayan ya kwashe tsawon okaci yana zaune a birnin Doha na kasar Qatar.
Baradar dai yana daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Taliban, tare da shugaban kungiyar na farko Mulla Umar, wanda ya mutu a cikin shekara ta 2013.
342/