5 Satumba 2021 - 09:19
Ayatullah Sayyid Mohammad Sa’ed Hakim Ya Rasu + Tarihin Rayuwar Sa

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA ya ruwaito, Ayatullahi Sayyid "Mohammad Sa’ed Hakim", daya daga cikin Maraji’ai abin koyi na Shi'a na Iraqi ya rasu yana dan shekara 86 a birnin Najaf Ashraf.

Sa’oin da suka gabata, Marja’in Taqlidin ya yi ban kwana da duniya kwatsam saboda bugun zuciya a Asibitin (Al-Hayat) da ke Najaful Ashraf.
Ayatullahi Hakim yana daya daga cikin Marja’oi hudu a Hauza ta Najaf. shi jikan diyar Ayatullahil uzma "Sayyid Muhsin Hakim", Marja’I abin kwaikwayon 'yan Shi'a a karni na goma sha hudu hijiriyya.

Tarihin Rayuwar sa:
An haifi Ayatullah Sayyid Mohammad Sa’ed Hakim a shekara ta 1314 bayan hijira a Najaful Ashraf. Mahaifinsa shi ne Ayatullah Sayyid Mohammad Ali Tabatabai Hakim kuma mahaifiyarsa ita ce babbar 'yar marigayi Marja’in Duniya gaba daya Ayatullah Haj Sayyid Mohsen Hakim.
Lokacin da ya cika shekaru 10, mahaifinsa ya kula da ɗansa da abin da yake dauke dashi na hikima, duk da neman ilimin kimiyya da koyarwarsa a manyan makarantu da makarantun firamare da amsa buƙatun mutane da biyan buƙatunsu, da kansa ya ɗauki nauyin renon ɗansa da karatu. ya koyar da shi kuma ya ilmantar da shi kuma ya raka shi zuwa matakan ƙarshe na manyan makarantun hauza.
Marigayi Ayatullahi Hakim, saboda da hazakarsa da kaifin kwkwalwarsa, hankalinsa mai aiki, da babbar himma, hikima da kaifin basira,sun sa ya wuce wadannan matakai cikin kankanin lokaci, a lokacin yana saurayi wanda ya shiga fagen karatun waje na huza kuma yana cikin dalibai na musamman Masu tunani da nazari ya maye gurben Ayatullahohi irin su marigayi Ayatullah Sayyid Mohsin Hakim da marigayi Ayatullah Haj Sheikh Husain Hilli da marigayi Ayatullahil Uzma Khoi.
Tun farkon kuruciyarsa, ya koyar da darussa masu girma na ciki da na waje kamar fikihu da Usul, da tafsiri da Akhlaq, Kuma a cikin da'irar koyarwa ta wannan Marji’i, akwai gungun mashahuran masana kimiyya da masu hankali, waɗanda a halin yanzu sune masu haskaka da'irorin Ilimi a makarantun hauza na Qum da Najaf.
Wannan babban malami, bayan kammala karatun hauza da koyan koyarwar addini cikin hauza ya isa matsayin ijtihadi, bai zauna a gida ba kawai yana fama da takarda da littattafai, sai dai yana daga cikin masu gwagwarmayar fuskntar Dagutai a lokacin Saddam. Ayyukansa da a ƙarshe suka kai ga shigar gidan yari a ƙasar na tsawon shekaru takwas.
Dalilin daure shi shine kokarinsa na kaddamar da karfafa gudanar da Tattakin Arbaeen a kasar Iraki; Don haka, yana daga cikin malaman fikhu na shari’a na Shi’a saboda laifin raya tattakin Arbain aka daurashe a kurkukun gwamnatin Ba’ath.

Bayan rasuwar Ayatullah Sayyid Abul Qasim Khui a shekara ta 1371 bayan hijira, Ayatullah Hakim ya bayyana marja’iyyaccinsa.
Marja’iyancin sa bai takaita a Iraki kan koyarwar addini da hauza kawai ba; Maimakon haka, ya nemi warware matsalolin duniya da na akidar 'yan Shi'a masu nisa ta hanyar aika gungun mashahuran addini zuwa yankuna da kabilun na masu nisa. Wannan Marja’i abin kwaikwayon 'yan Shi'a yana da ofisoshin wakailai a garuruwa kamar Najaf, Qom, Damascus da Beirut.
Marigayi Ayatullah Hakim, yana da littafan da anka buga 24 a cikin mujalladai sama da arba'in kan batutuwa kamar Fiqhu na Al'amuran Zamani da Wasu Al'amuran zamantakewa, kuma an fassara wasu daga cikin littafansa zuwa wasu harsuna, wasu daga cikinsun littafan Babban Marja’in Ayatullah Hakim gasu kamar haka:
1- Al’muhkam fi Usulil Fikh, (wannan gungun littafa ne dauke da juzu'i 6 tare da binciken muhawara kan Usul).
2- Dauratul fikhu na "Misbahul Minhaj", wanda sharhi ne kan fikihu na "Minhajus Salihin" na Sayyid Muhsin Hakim.
3- Littafin Risalah Ayatullahi Hakim - bayan yawaita buƙatun da bibiya kan nassoshi na malamai da mutane da yawa don yin koyi da su - an gabatar da shi wanna littafin a cikin mujalladi 3 mai suna "Minhajus Salihin".
4- Manasikul Hajji wa Umrah.
5- Babbarn sharhi akan littafi na Usul "Kifayah" na Akhund Khorasani a cikin mujalladi 3.

342/