2 Satumba 2021 - 12:55
Human Rights, Ta Yi Tir Da Korar Ma’aikata ‘Yan Yemen A Saudiyya

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Human Rights Watch (HRW), ta yi gargadi game da korar ma’aikata ‘yan asalin kasar Yemen a Saudiyya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Jami’a mai kula da bincike kan kasar Yemen, a Kungiyar ta Human Rights Watch, Afrah Nasser, ta bukaci gwamnatin Riyad, data dawo kan matakin na korar dubban ‘yan Yemen daga aiki tare da mayar dasu kasarsu dake fama da yaki da tabarbarewar al’amuran jin kai mafi muni a duniya.

A watan Yuli da ya gabata ne gwamnatin Saudiyya, ta fara aiwatar da matakin na kawo karshen aikin ‘yan Yemen ko kuma kin sabunta kwantaraginsu a cewar Kungiyar ta Human Rights Watch.

Matakin wanda ya fashi wasu kasashen duniya, ciki har da Yemen din ya haramtawa duk wani kamfanoni a Saudiyya daukar ma’aikata ‘yan Yemen da ya wuce kashi 25 cikin dari.

Kimanin ‘yan Yemen miliyan biyu ne rayuwa tare da yin aiki a kasar Saudiyya, a cewar al’akalumman gwamnatin Yemen na 2020, koda yake wasu an haife su a Saudiyya kuma basu taba komawa kasarsu ba.

Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin yakin da Saudiyya ta shelanta kan kasar ta Yemen, ya shiga a cikin shekarunsa na bakwai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gwamman dubban mutane tare da tilastawa milyoyi gudun hijira a cewar kungiyoyin kasa da kasa, yayin da MDD kuma ta danganta halin da ake ciki a Yemen da mafi muni a duniya.

342/