2 Satumba 2021 - 12:49
Kasashen Rasha Da Iran Sun Zama Zakara A Wasannin Sojoji Karo Na 6 Da Aka Kammala A Kudu Maso Gabacin Kasar Iran

Kungiyoyin wasannin sojoji na kasashen Iran da kuma Rasha ne suka zo na farko a gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa na shekara ta 2021, wacce aka kammala a yau Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : na kasar Iran ya bayyana cewa a yau ne aka kammala wasannin sojojin na wannan shekara a garin Konarak na lardin Sistan da Baluchestan daga kudu maso gabacin kasar Iran. Kuma ‘yan wasan kasashen Rasha da Iran ne suka zo na farko, a yayinda sojojin ‘yan wasa na kasashen Cana da Siriya suka zo na biyu da na uku a jere.

Wannan dai shi ne gasar wasannin sojojin ruwa ta kasa da kasa karo na 6, kuma manya –manyan jamia’an sojojin ruwa na kasashen Rasha, Iran , Siriya da Cana da wasu kasashe biyu ne suka sami halattar gasar daga ranar 31 ga watan Augusta zuwa yau 1 ga watan Satumba.

342/