Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Wata sanarwa da kwamitin ya fitar, ta kuma yi maraba da matakan da gwamnatin ta dauka na tabbatar da sun amfana daga hakkokin da suke da shi a matsayinsu na tsohon shugaban kasa da tsohon Firaminista.
Bayan maraba da matakin kwamitin yankin mai kula da mika mulki a Mali, ya kuma jaddada goyan bayansa kan mulkin rikon kwarya na kasar ta mali.
Nan gaba a mako mai zuwa ne ake sa ran babban mai shiga tsakani, na kungiyar ECOWAS, kan rikicin Mali, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, zai kai wata ziyara a kasar Malin.
342/