29 Agusta 2021 - 10:21
​Japan: Mutane 2 Sun Rasa Rayukansu Bayan Yi Masu Gurbataccen Riga Kafin Covid-9 Mai Suna Moderna

Gwamnatin kasar Japan ta tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu bayan an yi masu gurbataccen alluran riga kafin cutar Covid 19 na kamfanin Modrna daga kasar Amurka da aka yi masu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya ce mutanen biyu wadanda yan shekaru tsakanin 30-40 ne sun mutu ne bayan yin alluran riga kafin cutar ta Covid 19 na kamfanin moderna karo na biyu, jim kadan bayan an yi masu alluran.

A ranar Alhamis da ta gabat ce gwamnatin kasar Japan ta dakatar da amfani da gurbataccen alluran riga kafin na Moderna guda miliyon 1,630,000 wadanda ta rarraba su ga cibiyin alluran guda 863 na kasar.

Labarin ya kammala da cewa a halin yanzu ba’a da tabbacin cewa alluran ce ta kashe mutanen guda biyu, amma an san cewa an yi masu alluran kafin rasuwarsu. Don haka bincike ne zai tabbatar da abinda ya kashe su.

342/