29 Agusta 2021 - 10:20
​Iran: Harkokin Kasuwanci Tsakaninmu Da Afganistan

Kakakin kungiyar kamfanoni masu fitar da man fetur da dangoginsa zuwa kasar Afganistan daga nan Iran ya bayyana cewa harkokin kasuwanci na ci gaba a kan iyakokin kasar da kasar Afganistan kamar yadda aka saba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya nakalto Hamed Husain kakakin kungiyar kamfanonin man fetur da dangoginsa ya na cewa, jami’an shige da fice na kungiyar Taliban ne suke kula da kan iyakokin kasar Afgansitan.

Labarin ya kara da cewa, an sawwaka shigar da kayaki daga kasar Iran zuwa kasar Afganistan, tare da ragin kudaden fito har zuwa kashi 70% ga wasu kayakin.

Har’ila yau labarin ya kara da cewa kofofin shiga kasar Afganistan daga kasar Iran na lardain “Khurasane Radawi” da na Khurasan Junubi duk a bude suke kuma harkokin kasuwanci suna tafiya kamar yadda ya dace.

342/