23 Agusta 2021 - 12:10
​Najeriya: An Samu Karin Mutane 1,064 Wadanda Suka Kamu Da Cutar Covid-19

Cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta kasa NCDC ya bada sanarwan cewa an sami Karin mutanen da suka kamu da cutar ta Covid 19 ne a jihohi 9 da kuma babban birnin tarayyar Abuja. Kuma Jihohin sun hada da Lagos mai mutane 776 da kuma Rivers da mutane 143.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Sauran jihohin sun hada da Ekiti 49, Kwara 33, Ogun 21, Benue 18, Abuja 5, Osun 4 da kuma Yobe 2.

NCDC ta ce jimillar mutanen da suka kamu da cutar tun bayan bullarta a shekarar da ta gabata ya kai 186,635 sannan jimillar wadanda suka rasa rayukansu sabota ita ya kai 2,260.

342/