Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Kakakin gwamnatin Chadin, Abderaman Koulamallah ne ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a jiya Asabar inda ya ce hakan wani ƙoƙari na shirin faɗa wanda zai yi daidai da tsarin da ‘yan ta’ddan suke amfani da shi.
Mr. Koulamallah ya ce duk da hakan dai Chadin za ta bar kimanin sojoji 600 a ƙas, yana mai cewa tun da jimawa aka shirya wannan tsarin bayan tattaunawa da jagorancin G5 din. Har ila yau Kakakin gwamnati ya ce har ya zuwa yanzu dai ƙasar Chadi tana nan daram kan shirinta na faɗa da ta’addancin. Chadin dai tana da dakaru 1,200 cikin tawagar da ƙasashen biyar na Sahel suka haɗa tun a shekara ta 2017 da nufin faɗa da ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da na ‘yan tawaye da suke gudanar da ayyukansu a wajen.
Kan iyakokin ƙasashe uku haɗa da tsakiyar ƙasar Mali suna daga cikin yankunan da ayyukan ‘yan tawaye da ‘yan ta’adda suka yi tsamari lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubun dubatan mutane kama daga sojoji da fararen hula.
342/