17 Agusta 2021 - 14:42
Zambia : Shugaba Edgar Lungu, Ya Amince Da Shan Kayi

Shugaban Zambia mai barin gado, 'Edgar Lungu, ya amince shan kayi a zaben shugabancin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : A wani sako da ya wallafa a shafins na Tuwita, Mista Lungu, ya sha alwashin mutunta kndin tsarin mulkin kasar, ta hanyar mika mulki cikin ruwan sanyi.

Ya kuma taya zababen shugaban kasar, Hakainde Hichilema murna.

Haka kuma ya godewa ‘yan kasar da suka bashi damar ya shugabanci kasar.

Jiya Litini ne hukumar zaben kasar ta Zambiya ta ayyana madugun ‘yan adawan kasar Hakainde Hichilema, a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a ranar 12 ga wannan wata na Agusta.

Hichilema ya kayar da M. Lungu a zaben inda ya samu adadin kuri’u sama da 2,8 yayin da Lungu ya tsira da kuri’u sama da 1,8.

A karo na uku kenan da M. Hichilema, dan shekara 59 ya fafatawa da Shugaba Lungu, a shekarar 2016 kuri’u dubu 100 ne suke tsakanin ‘yan takaran guda biyu.

342/