15 Agusta 2021 - 12:45
Kasashen Afrika Sun Samu Alluran Riga Kafin COVID-19 Miliyan 114

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC, ta ce kawo yanzu, kasashen Afrika 53 sun samu kimanin alluran riga kafin COVID-19 miliyan 114.

ABNA24 : Cikin rahotonta na mako-mako da ta fitar jiya, cibiyar ta ce an yi wa kimanin kaso 1.75 cikin dari na al’ummar nahiyar riga kafi.

Ta kara da cewa, an riga an yi amfani da allurai miliyan 77.3 na jimilar alluran miliyan 114 da kasashen suka samu.

A cewarta, kasashen 5 da suka hada da Morocco da Afrika ta kudu da Masar da Najeriya da Tunisia, su ne ke kan gaba wajen samun alluran riga kafin tare da yi wa al’ummarsu.

Yawan wadanda suka kamu da cutar a nahiyar ya haura miliyan bakwai, yayin da mutane 179,986 suka mutu, sai kuma sama da miliyan shida da suka warke.

342/