Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulɗa da Jama'a na Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da cewa: A mataki na 30 na aikin Sa’iƙa-wato tsawa, a matsayin mayar da martani ga kai hari ga mutane marasa laifi, tun daga safiyar yau, jirage marasa matuki maru rubdawa na sojoji da dama, sun kai hari ga na'urorin radar da wuraren da sojojin Amurka da ke tsugunna a sansanonin Al-Dhafra da Al-Minhad na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Haka nan, an sake kai hari ga na'urorin radar da cibiyoyin taro na sojojin ta'addanci na Amurka a sansanin Sheikh Isa na Bahrain, da ɗimbin hare-haren jirage marasa matuki na Arash.
Sansanin Al-Dhafra na ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin ayyuka na Amurka mai laifin ta’addanci a yankin, kuma tana amfani da shi don ayyukan sama, ganowa, sa ido, da kai dauki.
Ofishin Hulɗa da Jama'a na Sojojin ta jaddada cewa: "Kai hari ga yankunan zama da kuma kai hari ga bikin aure daga makiya, misali ne na bayyane na ta’addancin yaƙi kuma yana bayyana muguwar dabi'ar 'yancin ɗan adam na Amurka', kuma babu shakka, martanin mayaƙan sojoji ga waɗannan laifuka zai kasance mai fa'ida da girma da fadi."
………………
Ra'ayinka