ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na twitter a safiyar yau Asabar ya kuma kara da cewa, bayan tsare kudaden kasar Iran na tsawon shekaru 40 a halin yanzu da kotu ta bukaci a mayarwa kasar Iran kudaden gwamnatin kasar Burtaniya tana son Iran ta yi musayar kudaden da fursinonin kasar wadanda suke tsare a kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa kudaden dai asalinsu na sayan makamai ne wadanda gwamnatin sarki shay a biya na sayan sabbin makamai daga kasar Burtaniya, amma bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a shekara 1979 sai gwamnatin kasar Burtaniya ta ki ta bada makaman ta ki kuma mayarwa iran kudaden.
Wannan halin ya ci gaba har sai da kotu ta bukaci gwamnatin kasar ta mayarwa Iran kudaden, shi ne a halin yanzo Johson yake son Iran ta saki fursinonin kasar wadanda suke tsare a nan Iran kafin ta saki kudaden.
Daga karshe Iragchi ya bukaci burtaniya ta saki wadannan kudade, ba tare da biyewa gwamnatin kasar Amurka wacce take matukar adawan da kasar Iran ba.
342/