12 Agusta 2021 - 13:28
​Sudan Za Ta Mika Tsohon Shugaba Umar Albashir Ga Kotun ICC

Gwamnatin kasar Sudan ta sanar da cewa, ta yanke shawara za ta mika tsohon shugaban kasar Umar Hassan Albashir ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ministar harkokin wajen kasar Sudan Maryam Sadiq Almahdi ta fadi a yau cewa, sun tattauna tare da wakilin kotun manyan laifuka ta duniya Karim Khan a birnin Kahrtum, dangane da mika jami’an Sudan da suka aikata laifukan kisan kiyashi.

Ta ce wakilin kotun ta ICC ya yi lale marhabin da kyakkyawan hadin kan da gwamnatin Sudan take baiwa kotun, musamman ma dangane da batun bin kadun wadanda suka aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a kan al’ummar yankin Darfur.

Kimanin mako guda kenan da kasar Sudan ta zama mamba da ta rattaba hannu a kotun manyan laifuka ta duniya, inda gwamnatin Amurka ta yi lale arhabin da hakan, tare da bayyana cewa zai taimaka wajen gurfanar da wasu daga cikin tsoffin jami’an kasar a gaban kotun domin hukunta su.

Da dama dai sun yi imanin cewa, an tilasta sabbin mahukuntan kasar ta Sudan ne wadanda suke yin biyayya sau da kafa ga turawa wajen daukar wannan mataki, babbar manufar tilasta Sudan domin ta zama mamba a kotun duniya dai shi ne mika Albashir da mukarrabansa ga wannan kotu.

342/