ABNA24 : Kungiyar Sala da Paz mai zaman kanta, ta ce an tsara gudanar da matakan soji cikin watanni 3 masu zuwa, karkashin tawagar mai kunshe da kwararru a fannin aikin soji, da dakarun kasashen Afirka ta kudu, da Botswana, da Angola, da Tanzania, da Lesotho, a aikin da zai lashe kudi har dalar Amurka miliyan 12.
Da yake tsokaci game da shirin, shugaban Botswana, wanda kuma shi ne ke jagorantar sashen siyasa da tsaro da ayyukan soji na kungiyar SADC, Mr. Mokgweetsi Masisi, ya ce tawagar za ta yi tasirin gaske, kasancewarta irinta ta farko da aka tsara yadda ya kamata a matakin shiyyar.
Tun daga shekarar 2017 ne dai lardin Cabo Delgado mai arzikin iskar gas, ke fama da tashe tashen hankula daga kungiyar ’yan ta’adda, lamarin da ya haddasa mutuwar dubban jama’a, tare da raba kimanin mutum 800,000 da muhallansu.
342/