ABNA24 : A cikin wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar jim kaɗan bayan taron Majalisar Ministocin ƙasar da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin shugaba Mohamed Bazoum inda ta sanar da ɗaukar wannan matsayar na kafa wannan sansanin a jihar Diffa da ke maƙwabtaka da Tabkin na Chadi.
Sanarwar ta ce babbar manufar kafa sansanin ita ce ƙarfafa dakarun ƙasar a ƙoƙarin gwamnatin na kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a yankin Tafkin na Chadi.
Ana ganin gwamnatin za ta kafa wannan sansani a yankin na Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar sakamakon yadda yankin yayi iyaka da Nijeriya, Chadi da kuma Kamaru, da suke a matsayin tungar mayakan ƙungiyoyin ta’addancin nan na Boko Haram da ISWAP da suka addabi ƙasashen.
Jamhuriyar ta Nijar tana daga cikin ƙasashen da suke fama da ayyukan ta’addancin ƙungiyoyin ta’addanci da suka addabin waɗannan ƙasashe na sama da ma sauransu irin su Mali da kuma Burkina Faso da su ma suke maƙwabtaka da ƙasar ta Nijar.
342/